28 Yuli 2020 - 11:36
Kwamitin Bincike Ya Wanke Tsohon Gwamnan Bankin Raya Kasashen Afirka

Kwamitin bincike wanda aka kafa don binciken tsohon gwamnan African Development Bank(AfDB), Akinwumi Adesina ya kammala binciken sa sannan ya wanke shi daga dukkan zarge-zargen da aka masa kan yin ba dai-dai ba a lokacinda yake rike da shugabancin bankin na kasashen Afrika.

ABNA24: Jaridar Premium timnes ta Najeriya ta bayyana cewa mambobin kwamnitin binciken su ukku ne kuma sun hada da Mary Robinson tsohon shugaban Island, Hassan B. Jallow tsohon alkalin alkalan kasar Gambia da kuma Leonard McCarthy tsohon babban ma’aikacin a bankin duniya.

A cikin watan Jenerun shekara ta 2020 da muke ciki ne wasu suka tseguntawa shuwagabnnin bankin irin ayyukan da dai-dai ba wanda Adesani yayi har guda 16, amma wannan kwamitin ta wanke shi.

Sakamakon bionciken ya budewa Mr Adesina kofar shiga takarar zabe na zama shugaban bankin raya kasashen Afrika a karo na biyu.

342/